25 Faburairu 2026 - 09:21
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Tarwatsa Gidaje Biyu A Kudancin Lebanon Tana Mai Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta

Rundunar sojojin mamayar Isra'ila ta tarwatsa gidaje biyu a garuruwan kan iyaka a gundumar Nabatieh, kudancin Lebanon, ranar Talata, a ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta wadda ta fara aiki tun daga karshen shekarar 2024.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa na Lebanon ya ba da rahoton cewa wani rukunin Isra'ila ya dasa abubuwan fashewa a cikin wani gida a garin Houla, a gundumar Bint Jbeil, kuma ya tarwatsa shi jim kaɗan baya cikin tsakar dare. Hukumar ta ƙara da cewa an lalata wani gida makamancin haka a unguwar Khurza ta Aita al-Shab.

Mutane sama da 4,000 ne suka mutu kuma kusan 17,000 suka ji rauni a yayin harin da Isra'ila ta kae kai wa Lebanon, wanda ya fara a watan Oktoba na 2023 kuma ya rikide zuwa cikakken yaƙi kafin Satumba na 2024. Rikicin ya ƙare daga baya a wannan shekarar bayan yarjejeniyar tsagaita wuta fara aiki.

Duk da yarjejeniyar, sojojin Isra'ila na ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da hare-hare kusan kowace rana da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane. Haka kuma suna ci gaba da iko da tsaunuka biyar na Lebanon da suka kama a yakin da ya gabata, tare da wasu yankunan da suka mamaye tsawon shekaru da dama.

……………………………………………………..

Your Comment

You are replying to: .
captcha